Ƙasar Yarbawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Barka da Zuwa Ƙasar Yarabawa

Ekaabo sii ile Yoruba

You are Welcome to Yorubaland



Taswirar Ƙasar Yarabawa
Maapu ile Yoruba
Map of Yorubalnd.

Gabatarwa

Ƙasar Yarabawa wani yanki ce na duniya da ake samu a bigiren 6o da 9o na Arewacin Latitu (Latitude North) sannan kuma tana bigire na 2o30’ da kuma 6o30’ ta Gabas da Longitu (Longitude East).

Tana iyaka da jahar Neja (Niger State) daga Yamma-Maso Arewa. Ta Gabas kuma tana iyaka da ƙasar Jamhuriyar Bini; wato Kwatano (Benin Republic). Sai kuma Tekun Atilantika (Atlantic Ocean) da ta yi maƙwabtaka da ita ta ɓangaren Kudu.

Wannan ita ce asalin ƙwaryar Ƙasar Yarabawa da ta killace Jahohin Oyo, Ogun, Ondo, Lagos Osun da Ekiti waɗanda suke cikin ƙwaryar Kudu Maso-Yammacin Najeriya, da kuma Kwara da wani yanki na jahar Kogi da ke Tsakiyar Arewacin (North-Central) Najeriya.

Ƙasar a kewaye take da ruwan da ya haɗa da koguna, tafkuna da kuma teku. Abin da ya saka ta zama ƙasa mai lema ko danshi. Daga Yamma tana iyaka da kogin Neja (River Niger) ta can ƙasa da mahaɗar Kogin sannan kuma tana Kudu da Kogin Kwara wanda yake haɗewa da Kogin Neja. Dukkanin Kudancinta kuwa sarƙafaffun koguna ne da suke haɗewa da babban kogin Neja da kuma Kogin Volta waɗanda suke kwarara ta cikin ƙasar daga Arewa zuwa Kudu ta cikin surƙuƙin daji mai danshi daga ƙarshe kuma suke shigewa cikin Tekun Atlantika da ke gaɓar Kudancin baki ɗayan ƙasar.

Rabaran Johnson (1960), ya ce akwai yiwuwar cewa Turawa sun gano wannan yanki na Yarabawa ne daga Arewa ta hanyar Fatake ‘yan Arewaci masu fatauci ta Arewaci da kuma Tsakiyar Afirka (Northern and Central Africa) kasantuwar a tsofaffin takardun tarihin ƙasar an yi amfani da sunayen Hausawa da kuma na Fulani. Kamar yadda ya hikaito Bature Webster’s yana siffata yankin a kundinsa da cewa: “YARRIBA, Afirca ta Yamma, Gabas da Dahomey, mai faɗin murabba’in mil 70,000 (70,000sq miles), da yawan jama’a kimanin mutane miliyan biyu, babban birninta, KATUNGA”. Johson ya ci gaba da cewa waɗannan sunaye; Yarriba da Katunga, sunaye ne da Hausawa suke kiran Yarabawa da kuma Oyo da su.

Manazarta


Johson S. (1960). The History of Yorubas From the Earliest Times to the Beginning of the British Protectorate. Lowe and Brydone (Printers) Limited, London, N.W. 10.

Onadeko T. (2008). Yoruba Traditional Adjudicatory Systems. Department of English, Olabisi Onabanjo Uniɓersity. African Study Monographs, 29(1): 15-28, March 2008

Ogunbado, A. F. (2003). Islam and its Impact in Yorubaland. The Islamic Ƙuarterly. 57. 18.

Masarautun Ƙasar Yarabawa

Ijoba ile Yoruba
Kingdoms of Yorubaland




Kaɗe-Kaɗe


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub